Sunday, March 3, 2019

*DUNIYAR BOLLYWOOD*

#HappyBirthday32YearsAnniversary
#ShraddhaKapoor
Most Talented Beautiful And Versatile Actress of Bollywood <3
.
TAKAITACCEN TARIHIN JARUMAR
***********************************
.
3 March, 2019
~~~~~~~~~•
Ita Dai lWannan Gwarzuwa Mai Yayi Da Tauraruwarta Take Cigaba Da Haskawa A Harkar Fina-Finai Wacce Ta Xama "Super Star" A Dan QanQanin Lokaci, An Haifeta Ne A Ranar (3 March 1987) A Garin (Mumbai, Maharashtra, India) Wacce  A Yau Take Bikin Murnar Qara Shekara, Inda Take Cika Shekara 32 Cif-Cif A Duniya.
Jaruma Shraddha Kapoor Ta Kasance 'Ya Ga Tsohon Jarumi *Shakti Kapoor* Sai Mahaifiyatya *Shivangi Kolhapure.* Wacce Ita Ma Tsohuwar Jaruma Ce, Mahaifan Nata Sun Fito Daga Mabanbantan QabiLu Duk Da Kasancewarsu Na Mabiya Addinin *Hindu* Mahaifinta Ya Fito Ne Da Sananniyar Xuri'ar Nan Ta Ahalin #Punjabi Yayin Da Mahaifiyarta Kuma Daga Ahalin #Marathi Take.
Bayan Kyakkyawar Sura Da Kyawun Fasali Da Take Dashi, Jarumar Tana Da Basirar Rerawa Da Rubuta WaQa. Ta Fara Fitowa A Film Cikin Shekarar (2010) A Matsayin Mai Takewa (Jaruma/Jarumi) Baya A Cikin Film Din "Teen Patti" Inda Daga Bisani Da Fito A Matsayin Mai Jan Ragama A Film (Lead Role) Cikin Shekarar (2011) Cikin Shirin
"Luv Ka The End" Jarumar Ta Samu Yabo Nassara Gami Da Tarin Masoya Tun Bayan Fitowarta A Cikin Shirin Mai Bada Umarni *Mohit Suri* Shirin Da Ya Kasance Mai Launin Soyayya Mai Narkar Da Xuciyar Masoya Film Din Da Ko Baka Kallon Fina-Finan India Xaka Samu Labari Akansa Wato Dai Film Din Ya Shuhura A Duniya Baki Daya Shiri Mai Taken "Aashique 2" Inda Ta Fito Tare Da Jarumi *Aditya Roy Kapoor" Wanda Ya Fita A Cikin Shekarar (2013).
A Shekarata (2014) Jarumar Ta Rera WaQa Mai Dadin Gaske Cikin Shirin 'Ek Villain`. WaQa Mai Taken 'Galliyan'
Ta Fito A Cikin Fina-Finai Da Dama A Masana'antar Ta Bollywood Irinsu:
"‘Haider’, ‘A Flying Jatt’, ‘Ok Jaanu’, ‘Half Girlfriend’, ‘Haseena Parkar’ Da Dai Sauransu Wanda Ta Samu Nassarori Na Lambobin Yabo Kana Da Yabawa Da Ta Samu Akan Irin Yadda Ta Taka Rawarta A Cikinsu. Bayan Harkar Kafce Jarumar An Bayyanata A Matsayin "philanthropist" Wato Macece Mai Son Mutane Da Taimaka Musu. Ta Bangaren Karatu Kuwa Jarumar Tayi Karatunta A Makarantar "Jamnabai Narsee School" Wacce Dake Da Matsuguni A Birnin Mumbai, Bayan Ta Kammala Ta Shiga Wata Jami'a Mai Suna "Boston University" Dake Kasar (Amurka) Inda Shekara Daya Kachal Tayi Ta Fece! Daga Nan Kuma Sai Ta Tsoma Kafarta A Harkar Film.
Ga Wasu Daga Cikin Fina-Finanta
⭐Stree (2018)
⭐Haseena Parkar (2017)
⭐OK Jaanu (2016)
⭐Rock On 2 (2016)
⭐Baaghi (2016)
⭐Haider (2014)
⭐Ek Villain (2014)
⭐Gori Tere Pyaar Mein (2013)
⭐Aashiqui 2 (2013)
⭐Luv Ka The End (2011)
⭐Teen Patti (2010)
Jarumar Yanzu Haka Akwai Fina-Finai Guda 4 Da Ake Saa Ran Ganinta A Cikinsu Guda Daga Cikinsu Kuwa Shi Ne Shirin *Saaho* Wanda Za'a Ganta Da Tauraron BaahubaLii!!! Jarumin Da Aka Fi Sani Da Suna Dan Tawaye (Prabhas Raju).

NASSARORI DA TA SAMU
🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
Jarumar Ta Samu Gagarumar Nassara Ta Mussanman Inda Ta Lashe Lambar Yabo Ta *Most Stylish Youth Icon Award* (2016) Wacce Babban Gidan Jaridar Nan Na "Hindustan Times" Dake Kasar India Suka Bayar. Sanann Again Ta Sake Lashe Makamanciyar Irin Wanann Kyautar Amma Fa Ta *Most Stylish Reader’s Choice Awards Winner (Female, 2017),* Wanda Shima "Hindustan Times" Ne Suka Karramar Jarumar Da Wannan Kyauta Haka Zalika A Dai Shekarar (2017) Din Ne Wani Gidan Jaridar A Kasar Ta India Mai Taken "Navbharat Times" Suka Sake Karrama Jarumar A Matsayin *Most Stylish Youth Icon Awards Winner (Female, 2017)*
Yaayin Da Jarumar Ta Cigaba Da Samun Mabanbantan Lambobin Yabo A Mabantan Lokuta Wanda Hakan Ke Faruwa Sakamon Rawar Gani Da Take Takawa Ta Kere Sa'a, Ta Karbi Lamar Yabo Ta
*Lions Gold Awards*,
*Stardust Awards*,
*Hello Hall of Fame Awards*,
*BIG Star Entertainment Awards*,
*Star Guild Awards*,
*Global Indian Music Academy Awards* etc. Wanann Kadan Kenan Daga Nassarori Da Jarumar Ta Samu A Harkar Fina-Finai.

MUHIMMAN BAYANAI
••••••••••••••••••••••••••••••
Jarumar Takan Shafe Tswon Awanni 8 Tana Sharar Bacci Abunta Atisayen Motsa Jiki Da Kuma Rawa Jarumar Tayi Imani Dasu A Matsayin Abubuwa Dake Taimakawa Gargar Jikin Dan Adam Wajen Kare Lafiyarsa Da Cututtuka Ga Kadan Daga Maganganun Da Jarumar Tayi Akan Muhimmancin Atisayen Motsa Jiki A Gareta:
“Fitness is fun, so I sometimes go in for yoga and sometimes other activities. I work out daily for two hours. I am playing a character of a basketball player in my next film Half Girlfriend, so I also need to practice for that,”said Shraddha before the release of her film Half Girlfriend.
.
One of her techniques to stay fit is to dance daily. “I shut myself in a room, play loud music and dance for hours till my feet give up. As I already have a lean body, I don’t need to put in a lot of effort to keep fit.”
.
Even when Shraddha is on a holiday, she doesn’t miss out on her exercise “I make sure I dance one or two hours a day even on a holiday. Yes there are few days when you feel that you don’t want to do anything but I still step up and do it.”

Masana Sanin Halayya Da Zubin Halittar Bil Adama Sun Bayyana Cewa Jaruma Shraddha Kapoor Siffarta Ta Tsayi A Matsayin Tsaka-Tsiki Wato Ita Ba Doguwa Ba Kuma Baza'a Kirata Da Gajeriya Ba, Yayin Da Suka Bayyana Siffar Idanuwanta Da "Hazel Brown" Wato Kore-Kore Ruwan-Qasa-Qasa, Gashinta BaQi Ne (Black)
Addinin Hindu Shi Ne Addininta.
Ga Adireshin Jarumar Kamar Haka:-
{{Address7th Floor, Palm Beach, Gandhigram Road, Juhu, Mumbai}}

ABUBUWAN DA TAFI SO
************************
Launinkan Da Tafi So Sune "Yellow" Da "Purple" Jarumar Ma'abociyar Wasannin Motsa Jiki Ce Kamar Yadda Muka Ambata A Baya Domin Kuwa Ta Kasance Inda Sun Fita Da Qawayenta Takan Buga Wasan Kwallon Kwando "Basketball" Da Volleyball Da Sauransu...
Jaruman Da Tafi So Su Ne:
Mahaifinta: Shakti Kapoor, Amitabh Bachchan, Hrithik Roshan, Aamir Khan, Johnny Depp, Edward Norton
Jarumai Mata Kuma Da Tafi So:
Nutan, Waheeda Rehman, Padmini Kolhapure, Madhuri Dixit Nene, PeeCee Priyanka Chopra,
Film Din Da Tafi So: Pyaasa (1957)
Hollywood:
⭐The Shawshank Redemption (1994), ⭐Central Station (1998),
⭐The Godfather (1972),
⭐Monster (2003),
⭐Boys Don't Cry (1999)

©Rubutawa & Tsarawa
✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍
#YusufIsyakuTsamiyarKara
#YusufSultan

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

A YAU NE FILM DIN "TRIDEV" NA KARUMI ★SUNNY DEOL ★JACKIE SHROFF ★NASEERUDDIN SHAH DA (MUGAMBO) YAKE CIKA SHEKARA 30.

A Yau Lahadi Ne Babban Film Din Nan Mai Taken "TRIDEV" Da Ya Tara Dandazon Manyan Taurari Irinsu "SUNNY DEOL" A Cikinsa ...