Sunday, February 24, 2019

🎥RANA MAI KAMA TA YAU🎥

 🎬🎬🎬RANA MAI KAMA TA YAU🎬🎬🎬
.            ⬆^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^⬆
.
Abubuwa Da Suka Faru A Rana Mai Kama Ta Yau (24, February) A Masana'antar Bollywood, Masa'antar Shirya Fina-Finai Mafi QoLoLuwa A Kasar India Gaba Daya.
******************************************
Tare Da Ni
YUSUF ISYAKU TSAMIYAR KARA
*********************************

💢Idan Dai Bamu Manta Ba A Ranar Irin Ta Yau Ta Shekarar Da Ta Gabata 2018 Muka Iski Mummunan Labarin Mutuwar Tauraruwar Taurarin Jarumai Mata A Masana'antar Film Ta Kasar India Wato Jarumar Da Aka Fara Kira Da Suna Mai Daraja Na Kalmar (Super Star) Wato "Sridevi Kapoor* Mahaifiyar Sabuwar Jarumar Nan Jhanvi Kapoor Wacce Ta Fito A Cikin Shirin *Dhadak* 2018 Film Dinta Na Farko A Industry. Mutuwar Sridevi Ta Girgiza Duniyar Film Ta India Bama Iya Bollywood Ba Inda Manyan-Manyan Jarumai Daga Kowanne Sashe Suka Nuna ALhininsu Ainun Game Da Babban Rashi Da Sukayi Na Wannan Gwarzuwar Jaruma Da Tarihin " Indian Film Industry " Bazai Taba Mantawa Da Ita Ba. Ita Dai Wannan Mashahuriyar Jaruma An Haifeta A Ranar 13 August 1963 Inda Ta Mutu - 24 February 2018) Ta Kasance Jarumar Fina-Finai Da Tayi Aiki A Masana'antun Film Na Kasar India Kama Daga Telugu, Tamil,Malayalam, Kannada Da Kuma Uwa Uba Bollywood. Jarumar Ba A Iya Nan Ta Tsaya Ba Ta Lashe Lambobin Xinare Na Karramawa Da Dama Kama Daga *National Film Award* *Nandi Award* Da *Tamil Nadu State Film Award*  *Kerala State Film Award* Da Kuma *Filmfare Awards* Guda 3
Sai  Filmfare Awards South Shima Guda 3, Da Sauransu.


💢A Rana Mai Kama Ta Yau Ta Shekarar 1999 Jaruma Kajol Devgan Tare Da Masoyinta Ajay Devgn Suka Angwance A Matsayin (Ango/Amarya) Inda Suka Cika Shekara 20 Cif-Cif Da Yin Aure.

💢A Ranar Dai Mai Kama Ta Yau Ta Shekarar 1989 A Saki Shirin #Guru Na Jarumi Mithun Chakarborty Inda Shirin Ya Cika Shekara 30 Ras Da Fita Kasuwa Shirin Ya Kunshi Jarumai Irinsu...
*Sridevi
*ShaktiKapoor
*Nutan.              Da Sauransu...!


💢A Rana Irin Ta Yau Ta Shekarar 1984 Aka Saki Film Din Jarumi Jeetendra Mai Taken #YehDesh Wanda A Hausance Za'a Iya  Kiransa Da Suna = WANNAN KASA
Shirin Ya Kunshi Babban Jarumi Kamal Hassan Da Jaruma #ZeenatAman #VinodMehra Da Kuma #Sachin
A Halin Yanxu Shekaru Aru-Aru 35 Kenan Da Aka Shafe Da Fitar Film Din.

💢A Rana Mai Kama Ta Yau Ta Shekarar 1984 Wato Shekaru 35 Da Suka Shude Aka Saki Film Din Sharara Na Babban Jarumi #RaajKumar Da Kuma Tsohuwar Jarumar Da Ake Yiwa Inkiya Da (The Dream Girl) Wato *Hema MaLini* Mata A Wajen Dhramendra Mahaifi Ga Bobby Da Sunny Deol Bayan Su Akwai Fasihan Jarumai Irin Su:-
*ShatrughanSinha
*MithunChakraborty
*LaxmikantPyarelal
*TinaMunim
*Ranjeet

💢A Karshe Kafin Na Rufe Karshen Babin A Ranar Dai Mai Kama Ta Yau Ta Shekarar 1989 Aka Saki Film Din #DoQaidi Na Jarumi Sanjay Dutt Inda Ya Cika Shekaru 30 Cif-Cif Shirin Dai Ya Kunshi Jarumai Irinsu #AmrushPuri #Govinda #Neelam #Farka *Shakti Kapoor* Da S




auransu...  FAQAT!!!

  👇Mai Rubutu👇
▶#Yusuf_Sultan◀

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

A YAU NE FILM DIN "TRIDEV" NA KARUMI ★SUNNY DEOL ★JACKIE SHROFF ★NASEERUDDIN SHAH DA (MUGAMBO) YAKE CIKA SHEKARA 30.

A Yau Lahadi Ne Babban Film Din Nan Mai Taken "TRIDEV" Da Ya Tara Dandazon Manyan Taurari Irinsu "SUNNY DEOL" A Cikinsa ...